Mai karatu kafun mu fara karatu ya kamata kasan wannan , Yaren Kanuri yana daga cikin manyan harsuna masu tarihi a Najeriya da kuma yankin Afirka ta Yamma. Wannan harshe ya rayu tun zamanin daular Kanem-Bornu – ɗaya daga cikin tsofaffin dauloli da suka yi fice a tarihin musulunci da kasuwanci a nahiyar nan.
🔹 Me yasa ya kamata mu koyi Kanuri?
Kamar yadda Turanci ke da muhimmanci wajen sadarwa da duniya, haka nan Kanuri yana da matuƙar muhimmanci wajen sadarwa da gidauniyar al'ada, addini, da tarihin kabilar Kanuri. Wannan yare yana cike da hikima, karimci, da ladabi, wanda ke nuna girmamawa da tsaftar magana.
🔹 Yabo Ga Harshen Kanuri
Harshen Kanuri yana da lafazi mai laushi da sauƙin koyon nahawu, musamman idan ana fassara daga Hausa ko Turanci. Harshe ne da ke nuna asali da mutunci, kuma yana ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma. Kalmominsa na ɗauke da ma’ana mai zurfi, kuma yana da matuƙar tasiri wajen koyar da ilimi, wa'azi, da waƙa.
> “Duk wanda ya koyi harshen wata ƙabila, kamar ya zama ɗan cikin ta.” – (Hikimar Hausa)
🔹 Ƙarfafawa Ga Mai Karatu
Idan kai ba Kanuri bane, ka tabbata cewa koyon wannan harshe zai ƙara maka ƙima, musamman idan kana zaune ko aiki a yankunan Borno, Yobe, ko Nijar. Zai ba ka damar fahimtar mutane, tarihi, da al’ada. Idan kai kuma dan Kanuri ne, wannan dama ce ta gina kanka da yarenka, domin babu abin da ke ƙara girmanka kamar kare harshenka.
> Mutum ba ya rasa komai idan ya koyi sabon harshe, amma yana rasa ƙima idan ya bar nasa.
✅ Kammalawa
Fassarar kalmomi daga Turanci zuwa Kanuri da kake karantawa a nan, wata hanya ce ta tabbatar da cewa harshen Kanuri yana ci gaba. Kar ka tsaya a karatu kawai – ka rika amfani da kalmomin nan, ka koya wa wasu, ka haɗa su cikin hira, da kuma koya wa yara da matasa.
Harshen Kanuri amana ne, kuma kai ne mabuɗin ci gaban sa. Don haka muci gaba da karatu
Kalmaa done fatowa wuzǝna ma. Kalmonin Da Suke Dangane Da Gida
Misali
Door -- Cinna -- Ƙofa
Please close the door.
Martǝne cinna dǝ zanne.
Danna Allah ka rufe kofar
Window -- taga -- Taga
She opened the window.
Taga dǝ kazǝna
Ta bude tagar
Chair -- Kuris -- Kujera
I’m sitting on the chair.
Kǝla kuris-yen namgǝna
Na zauna akan kujera
Light -- Nur --- Haske
Turn off the light.
Nur dǝ yaje.
Ka Kashe hasken
Fan Fanka. Fanka
The fan is not working.
Fanka dǝ cidajim ba
🧍♂️ JIKIN MUTUM
TIYI KAMMA
Kalma Ma’ana Misali
Head -- Kǝla -- Kai
My head hurts.
Hand --- musko --- Hannu
Raise your hand.
Muskom hamne.
Ka daga hannu.
Eyes -- Shim -- Idanu
Close your eyes.
Shim nǝm zanne
Ka rufe idanun ka
Tired -- mbaro -- Gajiya
I’m tired today.
Ku adǝ mbarǝkǝna
Yau dinnan na gaji
Hungry -- Kǝna --Yunwa
I’m hungry, let’s eat.
Kǝna fayin, dane bǝri bikke
Ina jin yunwa, bari naci abinci
---
🕰️ Waktuwa cida
Lokaci da Ayyuka
Kalma da Ma’ana da Misali
Morning -- Suwa-- Safe
Good morning!
NDA watǝ
Ina kwana
Afternoon --- kausu --- Rana
Good afternoon
NDA dubdo
Ina wuni
Night -- Bine -- Dare
Good night.
Nda dubdo
Barka da dare
Eat --- bǝri bo -- Cin abinci
I want to eat now.
Bǝri bikkiya raakǝna kǝrma
Sleep -- Kǝnǝm -- Barci
I want to sleep.
Lengiya raakǝna
Ina son inyi barci
Work -- cida -- Aiki
I’m going to work.
Cidaro leyin
Zanje aiki
---
💬Manaa kunbarinne
Maganganun Yau da Kullum
Jimla da Ma’anarta
How are you?
Nda nyi kǝlewa?
Yaya kake/kike?
I’m fine, thank you.
Kǝlewa sǝlai askǝrngǝna
Lafiya lau, na gode.
What’s your name?
Ayi suwum?
Menene sunanka/sunanki?
I don’t understand.
Asungǝyi
Ban gane ba.
Please help me.
Alah gammaa wa banane
Don Allah taimake ni.
See you later.
Sai tusha
Sai anjima.
I don’t know.
Nonguyi
Ban sani ba.
---
📱Whatsapp au Internet lan mana
Yin Magana a WhatsApp ko Intanet
Message -- Wosi -- Saƙo
Call me
Wa bone
Ka kira ni
Send it
Zuwune sha
Aika shi
Wait a minute
Jene waktu ganaro
Jira ɗan lokaci
No comments:
Post a Comment