DA ƊUMI-ƊUMI:
Farooq Kperogi: Buhari Ya Rabu da Aisha Kafin Ya Rasu – Aisha Ta Dawo Da Sunanta Na Haihuwa
Shahararren marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran Najeriya da ke zaune a ƙasar Amurka, Farooq Kperogi, ya yi wani jawabi mai cike da kalubale ga yadda ake yada labaran da suka shafi Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa, Kperogi ya ce:
“Ana ta yada magana cewa Buhari ya umarci Aisha ta nemi afuwa a madadinsa daga 'yan Najeriya. Ban tabbatar da sahihancin hakan ba, amma abin da na sani shi ne, kafin rasuwar Buhari, tsakaninsu da Aisha babu aure – sun rabu."
Aisha Ta Dawo Da Sunanta Na Haihuwa
Farooq Kperogi ya ƙara da cewa Aisha ta dawo da sunanta na haihuwa, wato Aisha Halilu, alamar cewa babu aure tsakaninta da Buhari a hukumance. Ya kuma nuna alamun rashin zumunci tsakanin su lokacin da Buhari ya yi ritaya zuwa Daura inda Aisha bata je ba, kuma daga bisani Buhari ya koma Kaduna shi kaɗai.
Maganar Rashin Lafiya a London
Kperogi ya bayyana cewa lokacin da Buhari ya kamu da rashin lafiya a London, an ce Aisha ta ƙi zuwa kulawa da shi, saboda bata kasance matar aurensa a lokacin ba. Daga bisani ne kawai ta je, bayan “tsananin lallashi”.
Tambaya Kan Jawabinta
Ya ƙare da cewa:
“Ina son sanin lokacin da Buhari ya umurce ta da ta nemi gafara ga 'yan Najeriya. A ina ta yi wannan magana? A wane lokaci? Me ya tabbatar da hakan?"
📰 Asalin rahoto: Farooq Kperogi (via Facebook)
No comments:
Post a Comment