Subscribe Us

Breaking

Friday, July 4, 2025

Fasihin matashin lauya mai zaman kansa, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya bayyana matsayinsa kan al’amuran siyasar Najeriya

Fasihin matashin lauya mai zaman kansa, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya bayyana matsayinsa kan al’amuran siyasar Najeriya, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda ake tafiyar da siyasa a ƙasar, da kuma bukatarsa ta ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai zarce a 2027 ba. A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, Baristan ya soma da cewa: > "Babu yadda za ka baza hajarka a kasuwa, kana kuma kushe hajjar wani domin naka ya ci kasuwa. Kamata ya yi ka tallata naka ko manufarka ta yadda za ka jawo hankalin jama’a da riba." Daga nan ne ya shiga bayani mai zurfi kan yadda wasu matasa ke kokarin kafa sabuwar jam’iyya ba tare da fahimtar tsarin siyasar Najeriya ba. Ya caccaki yadda wasu ke soke jam’iyyar ADC, inda ya ce: > "Jariri zai yi fada da babba! Na yi mamaki matuƙa. Ku da ya kamata ku fara tallan jam’iyyarku, ku bazama neman jama’a, amma sai kun barke da soke-soke da cin mutuncin wasu.” Barista Hamza ya jaddada cewa siyasar Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, yana buƙatar haɗin kai da tsari mai ƙarfi. A cewarsa: > "Dole sai an haɗa ƙarfi da ƙarfi, an haɗa mai gaskiya da mara gaskiya, mai adalci da wanda bai da ita, kafin a cimma nasara. Haka aka yi lokacin da aka haɗa Buhari daga CPC zuwa APC." Daga ƙarshe, ya bayyana cewa: > "Ni bana cikin kowace jam’iyya, amma bukata ta ita ce bana son in ga Tinubu ya zarce. Gwanda na zabi Peter Obi akan Tinubu. Amma dole sai an samar da jam’iyya mai ƙarfi da shiri na gaske kafin hakan ya faru." Ya kammala da cewa duk da yana fatan samun sabuwar tafiya, bai ga wata alamar haske daga waɗanda ke ƙoƙarin jagorantar sabuwar jam’iyyar ba, musamman ganin cewa da yawa daga cikinsu ba ma suna zaune a Najeriya ba, kuma dukansu 'yan Arewa ne. --- 📰 Asalin rahoto: RARIYA

No comments:

Post a Comment