Subscribe Us

Breaking

Saturday, April 12, 2025

TARIHIN KANURI PART 4

##**Harshen Kanuri yana cikin harsunan da ake amfani da su wajen koyarwa a makarantun firamare, musamman a yankunan Arewacin Najeriya da kuma makwabciyarta Nijar.


 Bugu da ƙari, harshen yana da matuƙar muhimmanci ga al'ummar Kanuri, har ma an ƙirƙiri shirye-shiryen ilimi don ba da damar yin karatu a cikin harshen har zuwa manyan matakan digiri na jami'a, ciki har da digiri na uku (PhD).**##

Yanzu da zaka tafi University na Maiduguri zaka samu acikin University din akwai course mai zaman kansa na koyon kanuri kamar yadda na fada har matakin Digiri na uku ana zuwa ,


Amma sai dai a yanzu kadan ne daga cikin mutane suke wannan karatun , wasu lamurran ne su ka yi musu yawa wasu kuma daman basu bashi muhimmanci ba


To Amma yanzu ni na saukakawa mutane ina koyar da su kanuri cikin sauki kuma a online kana zaune a cikin gida ba tare da wata matsala ba , Amma duk da haka fa zaka samu mutane dayawa suna sake wajan koyon yaren a hakan ,


Karatun yazo ya same har cikin gida, Amma sai ka samu mutum yana sake , Allah yasa mudace,


A cikin iyayen mu kanurai akwai ma wadanda basa goyon bayan na dinga karantar da mutane harshen kanuri saboda gudun kada wasu miyagu ko kristoci su koya, su zo su karantar da mutanen mu na kauye wasu bakaken akidu musamman addinin kristanci


Saboda dare da rana  makiya wannan yaren hari suke ta kaiwa ko ta ina da ina, to wannan shine dalilin su , don haka Allah ya kare mu ya kuma tsare mana imanin mu.



### **

No comments:

Post a Comment